A lokacin wani kasaitatcen taro da ya shirya domin murnar cikarsa Shekara gida da fara aiki a Najeriya, kamfanin Pop cola ya sha alwashin karade Najeriya baki daya.
Shugaban Kamfanin Hassan Mamuda ya bayyana haka a wajen taron bikin cikar kamfanin pop cola Shekara daya da fara aiki a Jihar Kano, Yana mai cewa sun yana alfahari da Jihar Kano da al’ummar Jihar da Yan Najeriya baki daya sabo da yadda suke cigaba da amfani da kayayyakin da kamfanin Maduda yake samarwa.
Yace suna samar da Biskit da Lemuka da ruwan Sha da Buhu da sarrafa fata da sauransu, Hassan Mamuda yace zasu cigaba da kyautatawa abokan harkokinsu da kwastomomi.
Anasa Jawabin Maitamakin Gwamnan Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, yace gwamnatin Kano tana alfahari da Kamfanin Pop cola sabo da yadda ya samarwa matasa dubu goma aikinyi da kuma samarwa Jihar Kano kudaden shiga.
Yana mai cewa yasan Hassan Mamuda tsahon lokaci mutumne Mai kwazo da kokari da tausayawa Al’umma, Dan haka kafaninsa na pop cola yake samun gagarumin cigaba.
Manyan Yan kasuwa da Yan siyasa da Yan uwa da abokan arziki suka halarci taron cikar kamfanin pop cola Shekara daya da fara aiki a Jihar Kano.

Leave a Reply